Faransawa na tunawa da harin Paris
November 13, 2017Talla
An dai tsaurara matakan tsaro yayin wannan biki na jimami da ya sauya makomar kasar ta fiskar tsaro tun bayan harin 13 ga watan Nuwamba shekarar 2015. Ba a dai samu mutane da yawa da aka tsammata ba da suka fita bikin wannan juyayi.
A wajen filin wasa na kasa Stade de France, Macron da mukarrabai da suka rufa masa baya sun ajiye furanni don tunawa da mutum na farko da ya fara halaka a harin , yayin da a sauran wurare da aka kai hare-hare da suka hada da wani wajen shan cafe a birnin na Paris inda aka halaka mutane 29. Akwai kuma iyalai da dama da suka hadu a gaban ginin wajen rawa na Bataclan domin tunawa da 'yan uwansu.