Gangamin goyon bayan kanana ga hukumomi a Faransa
July 3, 2023Jama'a sun yi dafifi a manyan gine-gine a duk fadin kasar Faransa a wannan Litinin don nuna goyon baya ga kananan hukumomi shida da gwamnati ta dauki matakan tsaro a cikinsu tsawon kwanaki shida, biyo bayan tashe-tashen hankula sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi wa wani matashi dan shekara 17.
Rikicin, wanda bisa dukkan alamu ya fara lafawa daga daren jiya, ya kunshi matasa ne da ke wadannan yankunan na bayan gari wadanda kuma akasarinsu baki ne da ke da tushen wasu kasashe Afirka, suna zargin gwamnatin Faransan da nuna wariya a kansu.
Ma'aikatar harkokin cikin gida na Faransar ta shaidar da cewar, a yayin tarzomar wajen manyan dakunan taro 99 aka kai wa hari, tare da sauran jama'a gine-gine. A yau ne Shugaba Emmanuel Macron na Faransar ke ganawa da magadan garuruwa 220 daga sassan kasar.