Fararen hula 30 sun mutu a harin Siriya
September 10, 2017A rahoton da Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights ta fitar a wannan Lahadi ta ce fararen hula akalla 34 sun mutu a hare-haren sama cikin su har da yara kanana. Rayukan da suka salwanta inji sanarwar kungiyar wasu iyalai ne da ke kokarin fita daga inda ake barin wuta da sojojin kawance suka kaddamar kan mayakan kungiyar IS a yankin na Deir al-Zour mai albarkatun karkashin kasa, yankin ya fada hannun kungiyar a shekarar 2014 inda ta ci gaba da iko da birnin kafin wannan makon Amirka ta jagoranci farmakin fatatakar mayakan da ayyukansu ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane a kasar.
A daya bangaren kuwa Sojojin gwamnatin Siriya a wannan Lahadi sun sanar da nasarar kwace da'ira ta karshe na zirin da ya hade gabashin birnin na Deir al Zor, da wannan nasara dai yanzu dukkanin hanyoyin sun dawo karkashin sojojin gwamnati a karon farko cikin shekaru.