Fararen hula na ci gaba da kauracewa Aleppo
November 30, 2016Talla
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan De Mistura, ya ce kwamitin tsaro na majalisar, zai yi ganawar gaggawa a birnin New York na Amirka a kan makomar fararen hula da hare-haren ke ritsawa da su a gabashin birnin na Aleppo. Kungiyar ba da agaji ta duniya wato Red Cross, ta nunar da cewa mutane 20,000 ne tsananin hare-haren da dakarun Siriyan ke kaiwa 'yan tawayen ya tilastawa barin gidajensu cikin kwanaki ukun da suka gabata.
A yanzu dai karbe yanki na uku mafi mahimmanci a Aleppo da dakarun gwamnatin Siriya suka yi, na nuna irin cikas mafi girma da 'yan tawayen suka fuskanta, tun bayan da suka fara tada jijiyoyin wuya tsahon shekaru biyar din da suka gabata.