1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya

January 4, 2024

Al'umma na kokawa kan yadda farashin kayayyakin abinci ke hauhawa a kasuwannin Najeriya, lamarin da ke jefa su cikin mawuyacin hali. Dama FAO ta yi hasashen cewar matsalar tsaro da matsin arziki za su dagula harkar noma.

Hatsi na daga cikin abincin da farashi ke hauhauwa a arewacin Najeriya
Hatsi na daga cikin abincin da farashi ke hauhauwa a arewacin NajeriyaHoto: Abdurrahman Kabir/DW

Hauhawar farashin kayayyakin abincin na zuwa ne bayan wani rahoto da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar dinki Duniya FAO ya yi hasashen cewa tsadar abinci a Shekarar 2024 zai zarta na Shekarar da ta gabata.  Tuni ma mazauna wasu jihohin Arewa ciki har da Katsina irin su Ya'u Tanimu suka fara shaida hauhawar farashin masara a kasuwa.

Karin bayani: Najeriya: Barazanar karancin abinci

Al'ummar Najeriya musamman na jihohin Arewa maso yammacin Kasar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga suka ce matsalar hauhawr farshin ta fi addabar su saboda 'yan bindiga sun hana su noma sakamakon hare-hare da garkuwa da mutane.Su ma mata da ke himadar girka abinci irin su Jamila Umar Musa suka ce tabbas sun fara ganin canjin cimaka a gidajensu sakamakon hauhawar farashi.

Mata sun shaidar da sauyi a fannin cimaka sakamakon tsadar abinciHoto: Abdurrahman Kabir/DW

Karin bayani: Neman mafita ga karuwar talauci a Najeriya

Babbar fargabar da 'yan Najeriya ke karawa ita ce yadda abinci ke tsada duk da cewar suna rayuwa cikin matsaloli na karancin kudi.Shinkafa da ke zama abincin yau da kullun ya karu da kusan 73%, duk da cewa har yanzu lokacin girbi ne a Najeriya. Dama wani sabon rahoto FAO ya bayyana yiyuwar hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya a 2024, sakamakon rashin tsaro da faduwar darajar kudi.



.