1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farashin alkama na karuwa a duniya

Becker, Andreas ZMA/AH
March 15, 2022

Farashin alkama da sauran kayan abinci na kara ta'azzara, talakawa a kasashe masu tasowa suna fuskantar barazanar yunwa.

Ukraine Ernte Donetsk Getreide
Hoto: Valentin Sprinchak/dpa/TASS/picture alliance

A kowace rana farashin alkama na kara tashi. A Chicago da ke zama cibiyar kasuwar kayan amfani gona mafi girma, farashin alkama ya karu da kaso 50 cikin 100, fiye da lokacin da Rasha ba ta afka wa Ukraine ba. Ana danganta wannan matsalar da kasancewar kasashen biyu masu yaki da juna cikin jerin manyan kasashe da ke fitar da alkama zuwa ketare. Yawancin alkamar da ake nomawa a fadin duniya dai, ana amfani da su ne a inda ake nomawa, kana abun da ya rage a fitar zuwa kasuwannin kasashen ketare.

Matin Qaim masanin tattalin arziki da harkokin noma ne, kuma darekta a cibiyar ci-gaban bincike a Bonn: "Rasha da Ukraine suna da kaso mafi girma na daya daga cikin uku na alkamar da ake fitarwa ketare. Rasha ce ke kan gaba, sai Ukraine a matsayin na biyar, sai kuma kasashen Amurka da Canada da Faransa. Don haka wannan babbar matsala ce a fannin abinci."

Rasha da Ukraine na fitar da hatsi zuwa kasashen duniya, idan yaki ya dore shuka da girbi ba zai yiwu ba a Ukraine

Hoto: AP

Yawancin hatsi da Rasha da Ukraine ke fitar da su zuwa kasuwannin duniya a lokacin bazara ne da kuma damina, "don haka manyan matsalolin ba su zo ba tukunna" a cewar masanin harkokin noma da tattali Qaim. Wannan yakin ba wai zai kawo cikas wajen fitar da hatsi da ke da akwai zuwa ketare kawai ba ne. Amma idan yakin ya ci gaba, shuka da girbi ba zai yiwu ba kamar yadda aka saba, akalla a cikin Ukraine.

Hakan na nufin karin tashin farashin alkama. Wannan babbar matsala ce ga kasashen da alkamar ce cimakarsu, kuma daga cikinsu akwai kasashe masu tasowa da yawa da ke dogaro da abincin da ake shigarwa daga ketare. Kasashe kamar Masar da Lebanon na dogaro ne da kayan abincin da ake shigowa da shi daga ketare na wajen kaso 70 zuwa 90 cikin 100. Ita ma Kenya tana dogaro ne da sayen alkama da wasu cimaka daga ketare, kazalika Turkiyya da wasu kasashe masu yawa.

Akwai bukatar yin nazari dangane da batun cimaka a cewar kwararru idan ba haka ba duniya za ta fada cikin wadi na tsaka mai wuya

Hoto: Alexander Ryumin/TASS/dpa/picture alliance

A cewar masanin harkokin noma da tattali Qaim dai ba wai a kasuwar alkama kadai Rasha da Ukraine ke da aringizo a duniya ba, har ma da masara da man girki da makamantansu: "Muna ganin yadda farashi ke kara ta'azzara, ba wai na alkama kadai ba har ma na sauran cimaka. Kowa na kokarin ganin cewar lamura ba su yi karfi ba, sai dai abun takaici babu abun da yake canzawa. Hakan na nufin al'ummomin wadannan kasashen matalauta za su shiga wani hali na rayuwar kunci, kuma matsalar yunwa za ta karu."

Halin da duniya za ta tsinci kanta a ciki dai ya ta'allaka a kan wannan yaki da ke gudana tsakanin Rasha da Ukraine da yake cikin mako na uku. Akwai bukatar yin nazari dangane da batun cimaka a cewar kwararru, idan ba haka ba duniya za ta fada cikin wadi na tsaka mai wuya na karancin abinci.