Farashin mai ya fadi
March 10, 2026
Danyen mai Brent ya fadi da kusan kashi 10 zuwa kasa da dala 90 kowane ganga daya a kasuwannin Asiya a ranar Talata, bayan da ya kai dala 119.50, farashi mafi tsada da aka taba gani tun tsakiyar 2022.
Sai dai dakarun juyin juya hali a Iran sun cije, suna mai cewa Tehran ba Washington ba ne da za ta yi "hasashen karshen yakin" kuma ba za ta bari "lita daya na man fetur" ya bar yankin ba idan hare-haren Amurka da Isra'ila suka ci gaba.
Daga baya Mista Trump ya yi gargadi a shafinsa na Truth Social cew, Iran za ta fuskanci hare-hare har "sau 20 masu tsanani" idan ta cigaba da toshe jigilar mai ta mashigin Hormuz, wanda ke sarrafa kashi daya cikin biyar na albarkatun mai a duniya.
Tuni dai farashin ya fara ja da baya bayan Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wata ganawa da Mista Trump tare da musanyar shawarwari da nufin sasanta yakin cikin gaggawa, a cewar majiyoyi daga fadar gwamnatin Kremlin.
Shugaba Trump ya kuma ce Washington za ta yi dage takunkumin da ke da alaka da mai a kan "wasu kasashe", matakin da zai iya bude kofa ga kara sassauta takunkumi kan danyen mai na Rasha bayan waya da shugabannin biyu suka yi.
Takaddama kan fito da mai a Gabas ta Tsakiya ya ba wa kasashen Indiya da China, biyu daga cikin manyan masu amfani da makamashi, suna habaka siyan mai na Rasha. Amurka ta ce za ta ba da izinin yin irin wadannan sayayya ba tare da takunkumi ba har tsawon kwanaki 30.