Farautar Joseph Kony da ƙungiyar tawayensa ta LRA
April 7, 2013Dakarun sojin Uganda sunce zasu cigaba da farautar 'ya'yan ƙungiyar tawayen nan ta Lord's Resistance Army ko kuma LRA, a Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya duk da zargin da aka yi na cewa ta daina gudanar da ayyukanta a yankin.
Haka nan kuma sauyin gwamnati a Bangui ba shi da wani tasiri kan ƙudurin hukumomin Ugandan na neman zaƙulo jagorar ƙungiyar wato Joseph Kony, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, lokacin da take maimaita kalaman Francisco Madeira, manzon ƙungiyar Tarayyar Afirka kan wannan batu.
Manzo na musamman na Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya a Majalisar Dinkin Duniya Abou Moussa shi ma ya bada tabbacin cewa ƙasarsa zata yi iya ƙoƙarinta wajen ganin an gano Joseph Kony.
Rahotanni na nunar da cewa Joseph Kony na ɓuya ne a yankin da ke kusa da iyakar ƙasashen Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya, Sudan da Kudancin Sudan.
Kony da ƙungiyarsa da ta yi ƙaurin suna saboda amfani da ƙananan yara a aikin soji, da yanka gaɓoɓin waɗanda suka kama da ma fyaɗe da cin zarafin mata, ta yi shekaru 25 yanzu tana bijire wa gwamnatin Uganda.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal