1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Farautar 'yan Isra'ila a filin jirgin saman Dagestan

October 30, 2023

Dandazaon jama'a sun kutsa kai a filin jiragen sama na Makhatchkala dake Jamhuriyar Dagestan a Kudancin Rasha da nufin farautar 'yan kasar Isra'ila bayan samun labarin isowar jirgin da ke dauke da su.

Russland Flughafen Machatschkala in Dagestan von Mob gestürmt
Farautar 'yan Isra'ila a filin jirgin saman Dagestan Hoto: Ramazan Rashidov/TASS/dpa/picture alliance

Kafofin yada labarai na kasar Rasha sun ruwaito cewar jama'ar da suka hallara filin jirgin dauke da tutocin Falasdinu sun yi ta furta kalaman kyamar Yahudawa tare da yunkurin kutsawa cikin jirgin da ya taso daga Tel-Aviv babban birnin Isra'ila.

Karin bayani: Zanga-zangar adawa da hari a sibitin Gaza

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Rasha ta ce an rufe filin jirgin na wani dan lokacin tare da karkatar da saukar wasu jiragen zuwa wadansu filayen jirgin sama. To sai dai gwamnatin Dagestan mai al'umma galibi musulmi ta ce an shawo kan lamarin bayan da aka baza jami'an tsaro.

A daidai lokacin aukuwar lamarin, Isra'ila ta kira Rasha da ta bai wa 'yan kasarta kariya yayin da wasu kasashe ciki har da Amurka suka yi Allah wadai da zanga-zangar nuna kyamar Yahudawa.

Karin bayani: Yaki da kyamar Yahudawa

A baya bayan nan an kona wata cibiyar Yahudawa a birnin Nalchik da ke yankin Kabardino-Balkarie kamar yadda kamfanin dillacin labarai na RIA Novosti ya ruwaito.