1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana fargabar yaduwar wasu baiyanan sirri

Ramatu Garba Baba
March 31, 2021

Kasashe mambobi a kungiyar tsaro ta NATO sun shiga fargaba bayan da aka fallasa yadda wasu manyan jami'an gwamnatin Rasha da na Italiya ke musayar wasu takardu na sirri a tsakanin juna.

Belgien Brüssel | Mazedonische Flagge vor dem NATO-Sitz
Hoto: Government of North Macedonia

Takaddamar ta kunno kai a tsakanin kasashen Rasha da Italiya, bayan da aka soma yada wani hoton bidiyo da ke nuna wasu jami'an kasashen biyu na mika takardun sirri don karbar rashawa, takardun da ake zargin na Kungiyar tsaro ta NATO ne. Wannan al'amari ya harzuka Italiya inda nan take ta tisa keyar jami'an diflomassiyan Rasha Moscow.

Batun yanzu ya tayar da hankulan sauran kasashe mambobin na Kungiyar ta NATO kan hadarin da ke tattare da tsaron yankunansu.  A nata bangaren gwamnatin Kremlin ta ce,  za ta dauki mataki daidai da wanda Italiyan ta dauka na korar jami'an ba tare da mayar da martani kan zargin jami'in da aka gani a bidiyon ba.