Fargaba bayan harin 'yan Houthi a Saudiyya
October 12, 2026
Sojojin Saudiyya sun mayar da martani kan hare haren jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami na mayakan Houthi a Yemen.
Harin da Saudiyyar ta kai wasu gundumomi biyu a Sana'a babban birnin Yemen ya hallaka akalla mutum guda wasu sha biyu kuma sun sami raunuka a cewar ma'aikatar lafiya a yankin yan Houthi ke jagoranci.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar Anees al Asbahi ya ce harin wanda ya fada kamfanin gishiri ya kashe mutum daya da kuma jikkata wasu mutum takwas.
Harin na zuwa ne yayin da yan Houthi suka ci gaba da kai hare haren jirage marasa matuka kan Saudiyya.
Hukumar filayen jiragen saman Saudiyya ta ce an rufe filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh amma ba ta baiyana lokacin da za a ci gaba da ayyuka da zirga zirgar jirage ba.