Harin 'yan ta'adda ya haifar da rudani a Yamai
January 29, 2026
Yankin da aka kai harin a nan ne babban barakin sojojin saman kasar yake. Lamarin dai ya haifasr da tsoro da rudani ga mutanen unguwannin da lamarin ya afku kafin da gaggawa jami’an tsaron kasar ta Nijar su yi wa wajen kawanya.
Lamarin dai ya soma ne da wajejen karfe 12 na dare da mintin ashirin, inda harbi na farko mutanen da ake kyautata zaton yan ta’adda ne suka soma da wani babban makami da ya firgita al’umma, kafin daga bisani a soma ganin ruwan harsashe cikin iska suna dosar wannan babban kewaye na filin tashi da saukar jiragen saman a birnin Yamai.
Cikin wnnan dare dai mutane da dama sun fito domin gane wa idanunsu abubuwan da ke afkuwa yayin da wasu suka shige cikin dakunansu. Dukannin mutanen da ke zama a wannan babban kewaye na filin jirgi sun kasance cikin firgici inda kowa daga na shi bangare ya ga abun da ya gani.
Wata mata mai suna Halima Hinsa, ta ce lalle jiya basu yi barci ba ta sabili da wannan iftila’i : "To lalle dai jiya da dare bamu yi barci cikin kwaciyar hankali ba, mu duka gida muka tashi zaune kowa na karkarwa Allah kal ya kawomana irin wannan matsala kuma."
Bayan kimanin awa daya ne dai jami’an tsaron kasar ta Nijar da suka kurda suka yi wa 'yan ta’addan kawanya, suka samu dakile wannan hari wanda kawo yanzu babu wani bayani dangane da rasa rayuka ko jikkata, ko kuma wata babbar hasara da aka samu inda sanarwa ta gwamnati kadai ce za ta iya bada adadin abun da ya wakana wanda har lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa daga gwamnatin ta Nijar.
Amma kuma ga labarin da muka samu tun a cikin daren jami’an tsaro sun halaka da dama daga cikin 'yan ta ‘addan yayin da wasu kuma aka kame su, sannan kuma al’umma da sauran ‘yan fafutika suka fito domin nuna goyon bayansu ga sojoji tare da yin kira ga ‘yan kasa da su buda idanu a duk inda suke.