1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamnoni cikin fargaba a Najeriya

March 7, 2019

A baya dai an fi tsammanin samun tashe-tashen hankula a lokutan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta kasa saboda zazzafar siyasar da ake alakantawa da kabilanci da addini amma an samu akasin haka.

Nigeria Präsidentschaftswahlen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ana bayyana fargabar samun tashe-tahsen hankula a zabukan gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin a jihohin saboda yadda bangarori ke jan daga wajen ganin ko a mutu ko a yi rai sai sun ci zabe.

A baya dai an fi tsammanin samun tashe-tashen hankula a lokutan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta kasa saboda zazzafar siyasar da ake alakantawa da kabilanci da addini amma an samu akasin haka.

Sai dai yadda aka dauki zafi a wasu jihohin da ya kai ga amfani da matasa wajen tada hankula da kuma afka wa abokan hamayya ya sauya tunanin mutane da dama da ya kai ga wasu ma ke fargabar fita zabukan gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi.

Akwai jihohin da ke fuskantar barazana samun tashe-tashen hankula saboda yadda yanzu haka siyasar ta yi zafi abin da ke haifar da fargaba musamman ga mata da sauran masu rauni da ke tsoron fita runfunan zabe.

Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Misali a jihar Gombe da a baya ta yi kaurin suna wajen ta’addancin matasa da ake kira ‘yan Kalare a karshen makon nan an samu tashe-tashen hankula da ya kai ga lalata kayayyaki da kona wasu wurare da motoci a wani gangami a yakin neman zabe.

Ana zargin ‘yan siyasa na amfani da matasan wajen ba su kudi da makamai gami da muggan kwayoyi da za su gusar da hankulan su

Kokarin jin ta bakin jami’an tsaro kan shirin da suke yi gabannin wannan zabe ya ci tura. Amma a wata tattauanawa tsakanin Al-Amin Suleiman Muhammad da mukaddashin sifeta janar na ‘yan sanda mai kula da shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya kan zabukan nan Alh Usman Dilli ya ce ya dauki matakai da suka kamata inda kuma ya roki ‘yan siyasa da sauran jama’a su bai wa jami’an tsaro hadin kai a yi zabe lami lafiya.

Yanzu haka dai kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai na yin kira ga ‘yan siayasa da su martaba yarjejeniyoyin da suka sa hannu na tabbatar da yin wannan zabe lami lafiya inda suke nemi hukumomi su tashi tsaye don magance duk wata fargaba da ake fuskanta a wannan lokaci.

 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani