1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba game da makomar tsiraru a Siriya

July 5, 2011

Mabiya mazhabobi na addinai daban-daban da kuma tsirarun ƙabilu a Siriya na fargaba game da makomarsu idan har an kifar da gwamnatin Assad a ƙasar

Shugaba Bashar Al-Assad na Siriya da shugaban ƙungiyar Hizballah Hassan Nasrallah a gaban kushewar Sayyida ZainabHoto: picture alliance/ZB

A haƙiƙa dai in banda 'yar ƙaramar ƙasa ta Lebanon, kusan babu wata ƙasa a yankin gabas ta tsakiya dake da ƙabilu da mazhabobi na addini kamar Siriya. Kama dai daga Musulmi da kiristoci zuwa ga 'yan Alawi da Druz da Isma'iliya da ragowarsu. A ƙarƙashin daftarin tsarin mulkin ƙasar dai, Siriya dake tu'ammali da manufofin gurguzu tun shekaru gommai da suka wuce, ƙasa ce da ba ta haɗa siyasa da manufofi na addini. A cikin shekaru 41 da mulkinsu gidan Al-Assad ba su taɓa nuna wata wariya ta aƙidar addini ba. Sai dai kuma zanga-zangar adawar da gwamnati ke fuskanta ka iya rikiɗewa zuwa wata tashin-tashina ta addini da ƙabilanci, musamman ma dai dangane da tsiraru a ƙasar, in ji Volker Perthes, ƙwararren masani akan al'amuran yankin gabas ta tsakiya:

Duk da tsauraran matakan da jami'an tsaro ke ɗauka masu adawa da gwamnati na ci gaba da zanga-zangarsu a SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

"Babban abin da tsirarun ke fargaba shi ne ɓillar wani mummunan rikici da yaƙin basasa mai ɗorewa idan har an kifar da gwamnatin Assad, inda za a wayi gari aƙidar addini tana taka muhimmiyar rawa a kuma riƙa fuskantar faɗace-faɗace da matakai na ramuwa."

Ko da yake ba a fuskanci irin waɗannan matakai na ramuwa a ƙasashe kamar Tunesiya ko Masar ba, amma tana iya yiwuwa a ƙasar Siriya, in ji Volker Perthes. Waɗanda zasu fi fuskantar barazana su ne 'yan Alawi saboda shi kansa shugaba Assad ɗan Alawi ne. Bugu da ƙari ma dai Hafez Al-Assad da magajinsa Bashar Al-Assad sun ba wa 'yan Alawi muhimman muƙamai a gwamnati da soja da kuma hukumar leƙen asiri. Tun dai bayan ɓillar zanga-zangar ta adawa gwamnati a fadar mulki ta Damaskus ke iƙirarin cewar wasu 'yan tawaye ne dake cikin ɗamarar makamai ke adawa da gwamnatinsa kuma wajibi ne a murƙushe su da ƙarfin hatsi. Gwamnati na ɗora laifin ne akan wasu kafofi na ƙetare tare da zargin 'yan salafiya da masu fafutukar kafa shari'ar musulunci da wasu ɗaiɗaikun ƙasashe, abin da ya haɗa har da Lebanon. Kimanin kashi 70% na al'umar Siriya musulmi ne 'yan sunna, a yayinda 'yan Akawi da Druz da Isma'iliya suka kama kashi 20% sai kuma kiristoci kashi 10%. A baya ga haka akwai kiristocin Iraƙi da suka yi ƙaura zuwa ƙasar sakamakon barazanar da suke fuskanta game da makomar rayuwarsu a Iraƙi. A sakamakon haka da yawa daga cikin kiristocin Siriyar ke fargabar cewar zai zama tilas akansu su yi ƙaura zuwa ƙetare idan har an kifar da gwamnatin Assad, kamar yadda Kristin Helberg 'yar jarida kuma ƙwararriyar masaniya akan al'amuran Siriya ta nunar:

"Mutane na fargabar wani yamutsi da tashe-tashen hankulan da za a iya fuskanta kamar dai yadda lamarin yake dangane da maƙobciyar ƙasa ta Iraƙi."