1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan ganawar Putin da Lukashenko

Ramatu Garba Baba
December 19, 2022

Shugaba Volodymr Zelensky ya baiyana fargabar kara kai wa Ukraine farmaki a sakamakon ziyarar da Vladimir Putin ya kai wa takwaransa Alexander Lukashenko na Belarus.

Lukaschenko da Putin
Lukaschenko da Putin Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Zenkovich

A wannan Litinin, Shugaba Vladimir Putin ya isa birnin Minsk na kasar Belarus don gana wa da takwaransa Alexander Lukashenko, ziyarar ita ce ta farko tun bayan wanda ya kai a shekarar 2019. Tuni gwamnatin Ukraine da ma wasu kasashen duniya, suka soma baiyana ra'ayinsu na fargaba, kan ziyarar da akasarin kasashen ke yi wa kallo, na kitsa makarkashiyar kai wa Ukraine sabbin hare-hare da zummar samun galaba a yakin da ake gwabzawa a gabashin Turai.

An jima ana rade-radin cewa, Rasha na neman taimakon sojojin kasar Belarus, wace babbar aminiyar kasar ce a rikicinta da Ukraine, zargin da kakakin gwamnatin Kremlin Dmitry Peskov ya karyata.