'Yan gudun hijira na fuskantar barazanar yunwa
February 26, 2021Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubun dubatar al'umma da ke gudun hijira a yankunan gabashin Afirka ne ke fuskantar barazanar tsunduma cikin matsananciyar yunwa a wannan shekarar, wadanda abin ya fi shafa sun hada da 'yan gudun hijirar da yakin Tigray ya daidaita da na Somaliya da Kudancin Sudan da sauransu. A halin da ake ciki a yanzu a yankin kahon Afirka, a iya cewa hasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na samun karancin cimaka ga mazauna sansanonin 'yan gudun hijira a yankin na gabashin Afirka da ma wasu sassan nahiyar na daf da zama gaskiya, inda tuni mutanen suka fara mayar da ciyawa da ganyayyaki da ma wasu tsirrai cimaka.
Karin bayani: Me ke haddasa yunwa a Afirka?
Hakan bai rasa nasaba da rashin isar kayan masarufi a wasu sansanonin musamman inda wadanda yakin Tigray ya tilasta masu barin muhallansu da akalla suka zarce dubu dari biyu. Tun bayan barkewar fada tsakanin dakarun gwamnatin Habasha da masu rajin kare yankin Tigray, gwamnatin kasar ta hana masu bayar da agaji kai agaji ga wadanda yaki ya daidaita.
A can kasar Somaliya a sansanin 'yan gudun hijirar da ke kudu maso yammacin Baidoa, mazauna sansanin sun shiga wani mawuyacin karancin ababen masarufi. A Sudan kuma kimanin 'yan gudun hijira sama da dubu dari da hamsin ne suka yi kaura daga kasashe makwabta zuwa kasar da suka hada da kasashen Sudan ta Kudu da Habasha da Afirka ta Tsakiya tare da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango. Baya ga matsanancin karancin cimakar da Majalisar Dinkin Duniyar ta hasaso, mazauna sansanin na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka masu yaduwa musaman a wannan lokacin da ake fama da annobar Corona.