1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan sabbin hare-haren a yankin Niger-Delta

Uwaisu Abubakar Idris/GATMay 9, 2016

A Najeriya sabbin hare-hare kan na'urorin hako mai a yankin Niger-Delta a dai dai lokacin da shugaban kasar ya sanya hannu kan kasafin kudi ya haifar da damuwa kan illar da wannan zai iya yi ga aiwatar da kasafin kudin.

Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Hare-haren har sau biyu da aka kai a kan naurorin tura man fetir da ke nuna kama hanyar sake komawa ga kai hare-hare a kan harakar man fetur din tun bayan afuwar da gwamnatocin da suka gabata suka yi wa masu wannan aika-aika a yankin na Niger-Delta ya zama abin da ke tayar da hankali da tsoron sakamakon da zai iya samuwa ga sashin man Najeriyar.

Hoto: picture-alliance/dpa

Ana dai danganta wadannan hare-hare na baya-bayan nan da neman kame daya daga cikin madugun kungiyoyin da ke tada kayar baya a yankin watau Tompolo da gwamnatin Buhari ke yi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Sanin yadda Najeriya ta dogara kusan kacokam a kan man fetir a matsayin hanyar samun kudin shigarta da zai zama abin dogaro a yanzu ga gwamnatin da ke kukan rashin kudin da raguwar farashin man, tuni ya sanya nuna damuwar yadda kai tsaye zai iya shafar aiwatar da kasafin kudin kansa.

Hoto: picture alliance/dpa/dpaweb

A yayin da shugaban Najeriya ya ba da umurnin ga jami’an tsaro su shawo kan masu kai hare-haren ga al'ummar kasar na cike da fatan ganin an samu aiwatar da kasafin kudin sau da kafa a dai lokacin da matsalolin tattalin arziki suka sanya kasar a gaba. Lamarin da kuma ya soma haifar da fargaba a zukatan al'ummar kasar

A lokutan baya dai masu tayar da kayar bayan na yankin Niger-Delta sun kasance wadanda suka gurgunta harkokin hako mai a yankin kafin a kai ga shirin afuwar da har yanzu ake aiwatar da shi. A yayin da aka ambato sun ba da sharudda na dakatar da kai hare-haren, za’a sa ido a ga yadda gwamnati zata bullo wa lamarin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani