Zanga-zanga ta fadada a Najeriya duk da matakin gwamnati
October 13, 2020A Najeriya kungiyar kare hakkin jama'a ta CISLAC ta yi kashedin hatsarin da ke tattare da takadamar da ake ci gaba da yi a tsakani sifeto janar na rundunar ‘yan sandan kasar da hukumar kula da aiyyukan ‘yan sanda a kan batun daukan sabbin ‘yan sandan da kotu ta dakatar a dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar zanga-zanga ta neman yiwa daukacin aikin ‘yan sandan garambawul. Takadamar dai tsakanin sassan biyu da suke gudanar da harkokin ‘yan sandan a Najeriya da ta kai su ga shige da fice a kotunan kasar ta kawo cikas a kan shirin daukan karin ‘yan sandan da ake matukar bukatarsu saboda kalubale na rashin tsaro a kasar.
Karin Bayani: Najeriya: Murna bayan rusa rundunar SARS
Matakin baya-bayan nan kotu ta sake karbe ikon daukar sabbin ‘yan sandan daga hannun sifeto janar na Najeriya tare da mayar da shi ga hukumar kula da aikin ‘yan sandan, abin da ya dauki hankalin kungiyar ta CISLAC. Malam Auwal Musa Rafsanjani shine shugaban kungiyar ya bayyana abinda ke daga masu hankali. To sai dai ga Hajiya Naja'atu Bala Muhammad daya daga cikin mabobin hukumar kula da aiyyukan ‘yan sanda na bayyana yadda doka ta tsara lamarin.
A dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar zanga-zanga a Najeriya kungiyar datawan arewacin kasar ta bayyana bukatar lallai a yi wa daukacin tsarin hukumomin tsaro har da sauya manyan hafsoshin sojan kasar don kawo karshen kasha-kashen jama'ar da ake yi. Kungiyoyin kare hakkin jama'a dai na masu dagewar cewa dole ne a yi garambawul a kan daukacin aikin ‘yan sanda kamar yadda Mallam Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC ya bayyana. A bayyane yake a fili cewa Najeriyar na fuskantar kalubale mai yawa tun ma kafin batun rusa rundunar 'yan sanda da ke yaki da ‘yan fashi da ma matsin lamba na neman yi wa daukacin tsarin tsaron kasar garambawul.