1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nijar ta ce kura ta lafa a birnin Yamai

August 29, 2026

An tashi da jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a Niamey, bayan wani hari kan filin jirgin saman Diori Hamani da sansanin soja na Base 101. Gwamnatin ta yi kiran da a kwantar da hankali.

Nijar, Yamai I Rayuwar yau da kullum bayan boren soja
Nijar, Yamai I Rayuwar yau da kullum bayan boren soja Hoto: Balima Boureima/Anadolu Agency/picture alliance

Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar da suka yi bore sun kai hari filin jirgin saman Diori Hamani da fadar shugaban kasa a Yamai, lamarin da ya kaiga shafe sa'o'i ana jin karar harbe-harbe da ma fashe-fashe.

Hare-haren sun kuma sa gidan talabijin da rediyon gwamnatin kasar daina watsa shirye-shirye na wani dan lokaci.

Zuwa karshen safiyar ta yau, ma'aikatar tsaron Nijar ta ce dakarun gwamnati na ci gaba da kwato muhimman wuraren da aka kai wa hari. Sai dai majiyoyin tsaro sun ce har yanzu akwai sojojin da suka yi tawaye a filin jirgin saman, kuma lamura ba su gama fitowa fili ba.

Wannan dai shi ne sabon kalubale ga gwamnatin shugaban mulkin soja, Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya karbi mulki a juyin mulkin shekarar 2023 tare da alkawarin inganta tsaro.

Bayan gidan talabijin na kasa ya dawo watsa shirye-shirye, ya sanar da cewa sojojin da suka yi tawaye daga wani sansani a Yamai ne suka bude wuta kan wasu muhimman wurare a birnin, amma jami'an tsaro sun dauki matakan gaggawa na dakile lamarin.

Da farko dai an yi zargin yiwuwar kungiyoyin masu ikirarin jihadi ne suka kai harin, ganin cewa kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da IS sun taba kai hare-hare kan filin jirgin saman fararen hula da sansanin sojin saman kasar a baya.