Sudan: Fargabar aikata laifukan yaki
June 29, 2023An dai ga hayaki ya turnuke yankin da shalkwatar sojojin take a tsakiyar birnin na Khartoum a yini na biyu na bukukuwan idin babbar salla, duk da sanarwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu da ke yakar juna suka yi gabanin bukukuwan sallar. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, ta sanar da shiga tsakani tare da tabbatar da cewa bangarorin biyu na gwamnati da kuma 'yan tawayen RSF sun amince da sakin firsinonin yaki a tsakaninsu. Tuni ma dai sojoji 125 da kungiyar ta RSF ta kama suka isa cikin iyalansu bayan ta sake su, sai dai kuma har kawo yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa hare-haren RSF din da na Larabawan yankin Darfur da ke mara musu baya ka iya haifar da aikata manyan laifuka kan dan Adam.