1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Yaki da cutar kyanda

March 6, 2024

A jihar Kano da ke Najeriya, iyaye da dama sun dauki matakin zuwa asibitoci domin duba yara da ake tunanin sun kamu da cutar kyanda.

Yaki da cutar kyanda
Yaki da cutar kyandaHoto: DW

Yanayin zafi da aka shiga a jihar Kano, ya sa wasu iyaye mata na nuna fargaba cewa cutukan da 'ya'yansu ke fama da su, ko alamu ne na kyanda. A kullum iyaye da dama ne ke tururuwar kai 'ya'yansu asibitoci don a tantance su. Haka sakamakon barkewar cutar kyanda da aka fuskanta a jihar mafi yawan mutane a yankin arewacin Najeriya.

Asibitoci da dama a jihar ta Kano sun dukufa domin gano yara masu cutar da kuma tantancewa ganin a sallami wadanda ba su kamu da cutar ba. Jami'an kiwon lafiya sun tabbatar da samun yara da dama dauke da cutar yayin da ake ci gaba da daukan mataki. Jami'an kula da kiwon lafiya a jihar ta Kano sun nuna mahimmancin ga iyaye wajen kai yaransu rigakafi da kuma kai marasa lafiya zuwa asibiti.