1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar barkewar yakin basasa a Myanmar

April 1, 2021

A wannan Alhamis din ce za a gurfanar da tsohuwar jagorar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi a gaban kotu a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa rikicin kasar ka iya rikidewa zuwa yakin basasa.

Tahiland Bangkok | Myanmar Protest nach Militärputsch
Hoto: Mladen Antonov/AFP/Getty Images

Ana dai tuhumar Aung San Suu Kyi da wasu manyan laifukan da ka iya hana ta rike mukamai har karshen rayuwarta. Bayan ganawa da ita a karon farko ta kafar bidiyo, lauyoyin tshohuwar shugabar mai shekaru 75 sun ce ta na cikin koshin lafiya duk da tsareta da aka yi na tsawon watanni biyu.

Ana dai sa ran sauraron karar ya kasance takaitacce, kuma ya shafi bangarorin gudanar na shari'ar kawai. Yayin ganawar keke da keke a ranar Laraba da kwamitin sulhu na Majalisar Duniya Duniya ya yi, wakiliyar Majalisar ta mussaman Christine Schraner Burgener ta ce kofarta a bude take don tattaunawa da gwamnatin soji da ke ci yanzu a kasar, sai dai ta kara da cewa al'amura ka iya rincabewa idan har aka jira har lokacin da gwamnatin za ta magantu.

Myanmar ta kasance cikin rikici tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula a farkon watan Fabarairun da ya gabata, inda kawo yanzu fiye da mutane 500 suka rasa rayukansu a arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar.