1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Habasha ta dage zaben 'yan majalisun dokoki

April 1, 2020

Kasar Habasha ta sanar da dage zaben 'yan majalisun dokokin kasar da aka shirya gudanarwa a watan Agusta mai zuwa.

Äthiopien Unterzeichnung eWTP Hub
Firaministan Habasha Abiy AhmedHoto: DW/Y. Gebrezihaber

Sanarwar hukumar zaben kasar ta ce ta dage zaben saboda wannan annoba ta Corona da ke ci gaba da bazuwa a duniya. Sai dai kuma ba ta sanar da ranar da yanzu za a gudanar da zaben ba.

Ana kallon wannan zabe a matsayin zakaran-gwajin dafi ga mulkin Firaminista Abiy Ahmed  don tantance ingancin sauye-sauyen da ya kaddamar a shugabancinsa. Kawo yanzu dai mutane 25 ne Habasha ta tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus a kasar.