Fargabar yaduwar corona a fadar White House
October 3, 2020Kusan ba abin mamaki ba ne idan an ce shugaban Amirka Donald Trump ya kamu da cutar duba da yadda ya shafe watanni yana danne tasirin cutar, alal misali amsar da ya bayar ga 'yan jarida a cikin watan Maris na cewa "Shi bai damu da cutar ba" a yayin da yake ganawa da su a fadarsa ta White House. Kamuwar wani na hannun daman Trump da corona a baya ya janyo zaman fargaba da kila wa kalar kamuwar akasarin ma’aikatan fadar White House gami da manyan jami’an gwamnati da iyalansu duba da irin cudanyar da suke yi iri-iri, ba tare da daukar matakan kariya ba.
Akwai hadarin Donald Trump ya yada cutar ga jama'a Dr. Vin Gupta, daya daga cikin Likitoci masu sharhi kan al’amura a nan Amirika ya ce "Akwai babban hatsarin kara yada cutar a wurin da jama’a da ma duk wanda ya shiga jirgi daya da shugaban Amirka Donald Trump ya kamata ya killace kansa kwanaki 14, koda kuwa an taba gwada shi." Yiwuwar Covid-19 ta fantsama a majalisar dokoki duba da yadda ‘yan kwanakin nan aka sha yin tarurruka a tsakanin ‘yan majalisar da jami’an gwamnatin Trump abu ne da ka iya faruwa a cewar wani dan majalisar dokokin Amirka.
Yanzu haka jam’iyar Democrat na nuna damuwa ganin cewa a ranar Talata da aka yi muhawara tsakanin Trump da Joe Biden, dukkansu babu wanda ya sanya takunkumin kariya haka kuma Shuagaba Trump zai shafe akalla makwanni biyu ba tare da fita yakin neman kuri’a ba, kasa da wata daya kafin babban zabe.