1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na fargaba kan makomar zaben Najeriya

January 20, 2023

Manyan kasashen yammaci na Turai sun gargadi 'ya'yansu da su kaucewa ziyartar Najeriya a yayin zaben watan Febrairu.

Nigeria l Wahlurne, Junge Wählerin gibt ihre Stimme ab
Rumfar zabe a NajeriyaHoto: picture alliance / NurPhoto

Sannu a hankali dai damuwa tana ta karuwa ciki da ma wajen tarrayar Najeriya bisa karuwar tada hankali yayin zaben. A cikin awoyi 24 da suka gabata kadai dai an fuskanci fashewar bama bamai a dandalin yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Rivers ko bayan harbi da bindiga a yakin neman zaben PDP a jihar Edo.


Tuni dai da ma an yi nisa a cikin nunin yatsa a tsakani na masu takarar da ke dada nuna alamun mutuwa ko yin rai a cikin zaben da ke da tasirin gaske. Kuma ko bayan 'yan kwamitin da tun da farkon fari suka samo alkawarin zama na lafiya yayin yakin neman zaben da kila ma bayansa, Su kansu manya na kasashen yamma da ke kallon harkokin zabe na kasar sun damu.

Matasa a lokacin yakin zabeHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance


Kasashen tarayyar Turai ya zuwa Birtaniya da Australiya sun umarci 'ya'ya na kasashensu da su kaucewa kasar yayin zaben da ke dada nuna alamu na tada hankali a cikinsa. Ya zuwa yanzu dai kwamitin zaman lafiya a yayin  zaben  dai na can na wata ganawa da manya na masu takarar kasar a Abuja da nufin nazarin barazanar da ke iya shafa zaben.


Koma ya take shirin kayawa a kokarin kaiwa ya zuwa samar da shugabanni ga kasar dai sabuwar barazanar na iya shafar shi kansa sakamakon da masu mulkin na Abuja ke fatan amfani da shi su burge duniya.

Yadda ake murnar sakamakon zabe a bayaHoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa


Shugaba Buhari dai ya dauki lokaci yana alkawarin yin ingantaccen zabe cikin zama na lafiya. Alkawarin kuma dake iya samun cikas da karuwar zubar jini  cikin fagen siyasa ta kasar. Ita kanta faduwar gabar Turawan dai na iya tasiri bisa tagomashin sabbabin yan mulkin da tsarin zabe na kasar ke fatan samarwa.


Wannan ne dai karo na farkon fari da tsarin demokradiyya ta kasar ke haura 20 a shekaru na rayuwa,  cikin fatan kaiwa mahdi ga kasar da baya tasha ba dadi a cikin mulkin soja.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani