Najeriya da Nijar na fama da kalubalen rashin tsaro
October 22, 2015Talla
A da-dai lokacin da wa'adin da sabuwar gwamnatin Najeriya ta ce ta dibarwa kanta Domin kawo karshen ayyukan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram, hare-haren kungiyar na kara zafafa a jihohin Borno da Yobe a Najeriyar da kuma jihar Diffa a makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, abin da ke ci gaba da haifar da tsro da fargaba ga al'ummar yankunan da abin ya fi kamari.