1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar kai hare-hare yayin bikin Sallah

Ahmed SalisuSeptember 9, 2016

Yayin da shirye-shirye suka yi nisa na bikin sallar layya a sassan duniya daban-daban, jami'an tsaro a Najeriya na nuna fargaba ta samun hare-hare a lokutan bikin sallah.

Eid Al Fitr in Zinder, Niger
Hoto: DW/L. Malam Hami

Wannan batu dai ya sanya dakushe mararin sallar daga zukatan mutane sai dai kuma wasu da dama sun lashi takobin yin watsi da wannan barazana domin cigaba da shagugulansu kamar yadda suka dauki aniyar yi. Rundunar tsaro ta farin kaya wato SSS ce dai ta fitar da sanarwar yiwuwar samun farmaki na addanci yayin shagugulan. A daura da wannan rundunar 'yan sanda kasar ta ce ta shirya tsaf don ganin ba a samu wani tashin hankali ba kamar yadda kakakinta DSP Magaji Musa Majiya ya shaidawa DW inda ya ce jama'a su kawar da duk wata fargaba don sun shirya don tabbatar da bikin sallar ya tafi lami lafiya.

Can a Jamhuriyar Nijar ma dai ana nuna dar-dar dangane da abinda ka je ya komo yayin bikin sallar musamman ma dai a jihar Difa da ke fama da tada kayar baya ta Boko Haram, sai dai a hirarsa da Zaharadeen Lawan gwamnan na Difa Alhaji Mahaman Lawali Dan Dano ya ce sun yi shiri na ganin komai ya tafi ba tare da wani kalubale ba hasalima ya ce tuni aka karya lagon 'yan Boko Haram da suka addabi mutane a yankin don haka jama'a su kwantar da hankulansu domin a cewarsa komai zai wakana ba tare da fuskantar wani kalubale ba duba da irin kyakkyawan shirin da suka yi.

Yayin da kalubalen tsaro ke kokarin dakushe armashin sallar ta layya a wasu sassan Najeriya da Nijar, a Kamaru kuwa shirin sallar ake yi cikin jiran tsammanin wa rabbuka saboda mafi yawan al'umomin suna kukan rashin kudi. Wakilin DW Mamadou Danda da ya bibiyi yadda lamura ke wakana a lardin Arewa Mai Nisa ya ce dabbobi sun yi arha amma babu masu saye yayin da a share guda ya ce hukumomi sun dauki tsauraran matakan tsaro domin kare jama'a duba da yadda yankin ya sha fama da hare-hare na 'yan Boko Haram kamar a makociyar kasar wato tarayyar Najeriya.

Hukumomi sun ce za su tabbatar da tsaro yayin bikin sallah don magance kai hare-hareHoto: imago/Xinhua
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani