1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: AfD a zaben Saxony da Thuringia

Pieper Oliver MAB/L
August 28, 2024

Hasashen jin ra'ayin jama'a na cewa jam'iyyar AfD mai kyamar baki a Jamus, ka iya samun karin karfi a zabukan da za a gudanar a jihohin Saxony da Thuringia.

Jamus | Zabe | Saxony | Thuringia | AFD | Ci-rani | Fargaba
Duk da yawan jam'iyyun da ke shirin shiga zaben, akwai yiwuwar AfD a yi nasaraHoto: DesignIt/Zoonar/picture alliance

Wariyar launin fata na daga cikin matsalolin da baki 'yan ci-rani suka saba fuskanta a jihar Thuringia ta Jamus, inda a lokacin duba tikitin jirgin kasa ga misali Nour al Zhoubi 'yar Siriya ta kasance fasinja daya tilo da aka bukaci ta nuna ID ko fasfo da ke dauke da hotonta. Wannan ya sa ta yi buras da shi, ta yi barazanar kiran 'yan sanda. A matsayinta na mai ba da shawara a Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira, Al Zoubi ta ce ko taki ba za ta motsa daga garin Gera  da ta shafe shekaru shida ba ko da jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta lashe zaben jihohi a Thuringia. Zaben wadannan jihohi da yiwuwar nasarar AfD dai, na tsoratar da 'yan ci-rani da ke da zama a cikinsu amma ba dukan su ba. Karan tsana da ake dora wa baki na kara tsamari a jihar Thurungia da Saxony, kuma harin da bako ya kai a garin Solingen da ya yi sanadin mutuwar mutane uku na iya kara ruruta wutar yanayin da ake ciki a jihohin Jamus da za a gudanar da zabe. Ga Nour al Zhoub da ta fito daga Siriya, wannan na tilasta wa baki yin taka tsan-tsan kamar yadda ya faru a cikin Disambar 2023 lokacin da shugaban jam'iyyar AfD na Thuringia Björn Höcke ya yi kiran zanga-zangar adawa da baki a kowace Litnin. Amma ta ce za su fuskanci karin wariyar launin fata, idan AfD ta lashe zabe.

Shugaban jam'iyyar AfD a jihar Thuringia Björn HöckeHoto: dts-Agentur/picture alliance

Shi ma Ismail Davul da ke da zama a Dresden yana da irin wannan tunani, na fargabar samun nasarar AfD a zabe. Shi dai an haife shi ne a Turkiyya, kuma ya zo Saxony a shekara ta 2006 domin yin karatu. Daga bisani kuma ya shafe kusan shekaru 11 yana aiki da Majalisar Kula da Shige da Fice ta birnin. Da farko dai Davul ya kula da matasa baki, amma yana sauraron damuwar iyaye. A yayin da baki da dama ke nuna matukar damuwa game da yiwuwar nasarar jam'iyyar AfD a zaben Thuringia da Saxony, wasu sun kuduri aniyar zaben jam'iyyar ta masu tsananin ra'ayin rikau. Jam'iyyar ta AfD na tayar da hankali akai-akai kan 'yan gudun hijira, kuma ta yi kokari domin kalmar "hijira" ta samu karbuwa tsakanin jama'a. Özgür Özvatan masanin harkokin siyasa a jami'ar Humboldt da ke Berlin, ya ce AfD na jan masu jefa wa Erdogan na Turkiyya kuri'a da Jamusawan da ke da tushe da Rasha a jika domin cimma burinta. AfD na neman gaya wa baki masu jefa kuri'a cewe: A baya kuna aiki tukuru domin samun rufin asiri, amma a yanzu komai ana bai wa 'yan gudun hijira da sauran baki. Wannan batu na AfD dai, na zaman farfagandar siyasa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani