Fargabar sake aukuwar rikici bayan zaben Kenya
March 8, 2013A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan zaben kasar Kenya. A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne kamar haka: Zullumi na dakon sakamakon zabe a birnin Nairobi sannan sai ta ci-gaba da cewa.
"Yayin da aka samu jinkiri wajen kidayar kuri'u a zaben kasar Kenya, ana kara samun fargabar yiwuwar sake aukuwar wani rikici. A wani mataki na rigakafi, 'yan sanda na yin sintiri musamman a unguwannin marasa galihu dake gabacin Nairobi babban kasar, inda tun a tsakiyar mako komai ya tsaya cik ba ka ganin mutane a kan tituna, yayin da kantuna da makarantu suka kasance a rufe. Da farko dai hukumar zaben kasar ta so ayyana sakamakon zaben shugaban kasa a ranar Laraba, amma an samu jinkirin kidayar kuri'u, kuma ya kara sanya fargabar cewa ana iya sake samun aukuwar tashe tashen hankulan da suka biyo bayan zaben kasar na karshen shekarar 2007. Sai dai duk tangardar na'urar zabe da aka fuskanta, amsu sanya ido a zabe sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana."
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan zaben na Kenya inda ta ce:
"Matsalolin fasaha sun jinkirta ba da sakamakon zabe, abin da ya janyo kace nace game da aikin kidayar kuri'u, musamman shawarar da shugaban hukumar zabe Issac Hassan ya yanke ta shigar dukkan kuri'un da aka kada cikin lissafi wato har da wadanda suka lalace. Jaridar ta ce bambamtawa tsakanin kuri'un da aka kada da wadanda suke sahihai yana da wahala, domin kuri'un da da yawa daga cikin 'yan kasar ta Kenya suka jefa sun lalace kasancewar ba su fahimci sabon tsarin zaben kasar ba."
Tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya
Ita kuwa jarida die Tageszeitung tsokaci ta yi a kan harkar ilimi a tarayyar Najeriya tana mai cewa, mai za faru idan malamin firamare ya fadi a jarrabawar makarantun firamare? Ta ce a jihar Kaduna kashi uku cikin hudu na malamai sun fadi a jarrabawar karshe da ake wa 'yan aji hudu na firamare. Kamata yayi wadannan malaman sun lakanci matakin farko na lissafi da rubutu da kuma 'yar masaniya ta adabin Najeriya. Jaridar ta ce abin bai ba da mamaki ba domin a karshen watan Nuwamban bara, an gano malamai kimanin 2000 a Najeriya dauke da takardun shahada na bogi, sannan rabinsu ba su da kwarewar koyarwa a makaranta. Ta ce a da Najeriya na zaman jagaba a harkar ilimi a yammacin Afirka, amma yanzu harkar ilimi a kasar ta koma-baya."
Rashin ba wa fararen hula kariya a rikicin Kongo
Fararen hula ba sa samun kariya a fagen daga, har wa yau dai inji jaridar ta die Tageszeitung ta na mai nuni da halin da ake ciki a kasar Kongo, inda ta ce daruruwan mutane sun rasu a gumurzun da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da sojojin sa kai a wani yanki dake gabas da Kinshasa babban birnin kasar. Sojojin Majalisar Dinkin Duniya da aka girke a yankin don ba da kariya, sun kasa yin wani abin kirki na hana wannan ta'asar aukuwa. A wasu lokutan ma ana zargin su da korar wadanda lamarin ya shafa zuwa gidajensu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar