1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar sake barkewar cutar corona a Asiya

Abdullahi Tanko Bala
May 10, 2020

An sake samun sabbin kamun cutar corona a kasashen China da Koriya ta kudu da kuma Iran lamarin da ke barazanar mayar da hannun agogo baya a nasarar da aka samu a yaki da yaduwar cutar

China Wuhan | Hubei verringert die Corona-Alarmstufe
Hoto: Getty Images/AFP/Str.

Koriya ta kudu ta bada umarnin rufe dukkanin gidajen barasa da gidajen rawa a birnin Seoul bayan samun wasu gomman mutane da suka kamu da cutar coronavirus.

An danganta mutanen da suka kamu da cutar da wani wanda ya halarci gidan rawa a karshen makon da ya gabata.

Kasar ta nahiyar Asiya ta ruwato sabbin kamun cutar ta corona har mutum 34, karon farko da aka sami adadi mai yawa na karuwar cutar a cikin wata guda.

Mutane 10,874 ne suka kamu da cutar a kasar baki daya yayin da wasu 256 kuma suka rasu.

A halin yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar corona a duniya ya haura mutum miliyan hudu.