Fargabar samun rikici a zabukan 2015 a Najeriya
December 23, 2014Yadda lamura ke kai koma a fagen siyasar Najeriya ya sanya bukatar al'ummar kasar su kai zuciya nesa a zabukan da ke tafe domin gujewa abinda ya faru bayan zabukan da aka yi cikin shekara ta 2011 inda aka samu hatsaniyar da ta yi sanadin rasuwar mutane da dama da ma asarar dukiya mai yawan gaske.
To sai dai duk da irin fadakawar da ake yi, alamun rikicin na kara bayyana a tsakanin magoya bayan 'yan siyasa daban-daban. Wannan yanayi dai da ake ciki ga misali ya kai ga afkawa gwamnan Gombe da ke arewacin kasar Ibrahim Hassan Dan Kwambo wanda ya bukaci sake zaben shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda wasu al'ummar jihar ke ganin ya gaza.
Can a kudancin kasar kuwa 'yan kabilar Ijaw ta shugaba Jonathan ce ke fadin ko mutuwa ko yin rai ga duk wani kokari na tauye hakkin gwarzon nasu da suke yiwa kallon mai ceton da yai nisa ga kokari na kaisu tudun mun tsira. Wannan dai ya sanya masana harkokin siyasa a kasar ke hangen makoma maras kyau ga kasar muddin ba a kai ga dakile wannan ba cikin gaggawa.
Tuni dai aka fara yin kira ga jam'iyyun siyasar kasar da su yi yakin neman zabe ba da gaba ba sannan su ja kunnen magoya bayansu wajen yin abinda ya dace yayin da a hannu guda aka bukaci hukumar zaben kasar da su yi abinda ya dace a lokacin zaben musamman fidda sahihin sakamako wanda mafi akasari juya shi kan haddasa rikici.