1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYuganda

An jibge sojoji a kan hanyoyi gabanin zaben Yuganda

January 14, 2026

Da dama na fatan samun canji, yayin da wasu ke tsoron samun yamutsi da danniya, wasu kuwa ke son Shugaba Yoweri Kaguta Museveni da ke mulki tamkar na mutu ka raba ya yi tazarce.

Uganda Wakiso 2026 | Polizist setzt Pfefferspray gegen Anhänger von Bobi Wine bei Wahlkampfveranstaltung ein
Hoto: Hajarah Nalwadda/Getty Images

Halin da ake ciki ke nan a Yuganda gabanin zaben shugaban kasa da za a gudanar a wannan Alhamis 15 ga wannan wata na Janairu da muke ciki. Da dama na fatan samun canji, yayin da wasu ke tsoron samun yamutsi da danniya, wasu kuwa ke son Shugaba Yoweri Kaguta Museveni da ke mulki tamkar na mutu ka raba ya yi tazarce.

An hangi motocin sojoji sun yi kaka-gida a kan hanyoyin Kampala babban birnin kasar cikin shirin ko-ta-kwana, abin da ya haifar da tababab a zukatan al'ummar Yuganda da dama kan ko zaben zai gudana cikin lumana. Rabon da Yuganda ta samu damar mika mulki cikin lumana daga wata gwamnati zuwa wata, tun a shekara ta 1962. Al'umma na cikin dari-dari da kuma tarin damuwa, musamman ma da aka bukaci 'yan kasar da su bar rumfunan zabe da zarar sun kada kuri'asu. Wannan umurni ya sa mutane da dama kamar Maria Taremwa cikin shakku, inda take cewa:

"Yadda ake dukan mutane ababban birnin kasar musamman saboda wanda suka zabi su marawa baya ko kuma suke ganin ya fi cancanta da zama dan takara, abin tsoro ne. Mutane da dama na son zama su kasa su tsare su raka su kuma jira, abin da yasa ake dasa ayoyin tambaya kan umurnin. Ina fargabar samun hargisti bayan zabe, sai dai ina fatan ba za a katse Internet ba kamar a baya, ina tunanin an takaita amfani da kafar sadarwa ta Facebook a lokacin zaben da ya gabata."Shi ma Jacob Nuwashumbusha mazaunin Kampala ya yi gargadin barkewar rikici, koda yake ya ce:

"A matsayinmu na 'yan Adam, komai yana iya faruwa. Kowa da irin zuciyarsa, ganin yadda aka baza jami'an tsaro ya kamata mu yi karatun ta nutsu mu zauna lafiya. An jibge jami'an tsaro ne saboda tabbatar da zaman lafiya, ya za mu fassara hakan da kokarin tursasawa? Amma dai tilas akwai fargaba, ya kamata shugabanni su yi kira ga magoya bayansu kan zaman lafiya. A karshe dai, kowa na cikin fargaba, muna zaune ne tamkar a kan tsinin bindiga."

Shugaba Yoweri Kaguta Museveni na Yuganda da ke neman tazarce a karo na bakwai, ya dare kan madafun iko ne tun a shekara ta 1986. Mai shekaru 81 a duniya, ya samu wannan damar ne bayan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima tare da cire adadin shekaru ko wa'adin da shugaban kasa ya kamata ya yi a kan mulki.

Babban kalubalen Shugaba Museveni shi ne, abokin hamayyarsa Robert Kyagulanyi Ssentamu da aka fi sani da Bobi Wine. Mai shekaru 43 a duniya mawaki kana jagoran babbar jam'iyyar adawa ta National Unity Platform (NUP), na da goyon bayan matasa masu kada kuri'a. A yayin yakin neman zabensa, ya bayyana cewa wannan zaben, juyin-juya hali ne.

Hoto: Uganda PPU

Tun a shekara ta 2021 ya zamo fatan matasan kasar, kuma ya samu kaso 35 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Sai dai wanne fata ake da shi kan nasarar 'yan adawa a wannan zaben? Kwararru kamar Adolf Mabaine da ke sharhi kan al'amuran siyasa na da ra'ayin cewa:

"Suna da damarmaki sosai a bangarensu, shi ke da jami'an tsaro kuma shi yake nada wanda zai jagranci Hukumar Zabe. Yana da masu yi masa yakin neman zabe, kuma gwamnatin ta dan yi abin a zo a gani. A zahiri za a iya samun wadanda za su sake zabarsa. Ga 'yan adawa, abu daya ya kamata su yi wanda zai iya ba su nasara, shi ne su hade waje guda tare da tsayar da dan takara daya."

Sai dai ga Frederick Golooba Mutebi mai sharhi kan al'amuran siyasa a Yugandan, akwai tarin tambayoyi kan ko zaben zai gudana cikin gaskiya da adalci da ma sahihancin Hukumar Zaben. A cewarsa kusan kowanne zabe sai an samu rahoton magudi, wanda kuma ake zargin gwamnati da hadin bakin Hukumar Zabe da tafkawa, kuma duk da cewa gwamnatin ta sha musanta wannan zargi, babu aminci tsakanin mahukunta da 'yan kasa a kan zaben.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani