Burundi: Ana gudanar da zaben shugaban kasa cikin fargaba
May 20, 2020![Burundi Wahlen 20.05.2020](https://static.dw.com/image/53510163_800.webp)
Talla
Zaben wanda zai kawo karshen mulkin Pierre Nkurunziza, wanda ke kan mulkin tun a shekara ta 2005 wanda kuma ba zai sake tsayawa takara ba. Za a fafata tsakanin Janar Évariste Ndayishimiye na kusa da Nkurunziza, da kuma jagoran 'yan adawar Agathon Rwasa. Ana gudanar da zaben ne dai ba tare da halatar wakilai masu saka ido ba na MDD da kuma na kungiyar tarrayar Afirka ba AU, saboda gwamnatin ta Burundi ta ki ammincewa da su.