1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram na fadada sansani a Abuja

Uwais Abubakar Idris
September 7, 2020

Labarin kafa sansanonin na kungiyar Boko Haram a jihar Neja da kuma a baya bayan nan wasu yankuna da ke kusa da Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na cigaba da tada hankalin 'yan kasa.

MNJTF Multinational Joint Task Force
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Kasa da watanni biyu da samun labarin kafa sansani na kungiyar Jama’atu Ahlu Sunnah Li Da’awatti Waljihad a jihar Neja sai gashi a yanzu kuma an sake ambaton hukumar kwastam na cewa kungiyar ta kafa wasu sabbin sansanoni a wuraren biyar da suka da da gandun Rubochi da ke kusa da Gwagwalada a Abuja da kuma dajin kunyam da ke kan hanyar zuwa filin jiragen saman Abuja da kuma dajin kwaku da ke karamar hukumar Kuje a Abuja.

Wannan na nuna kara matsowar yayan kungiyar zuwa Abujan babban birnin tarayyar Najeriya da bisa al’ada aka san yana da cikakken tsaro.  Matakan da mahukunta suka dade suna bayyana cewa suna dauka domin kawo karshen Boko Haram   

Tuni dai hedikwatar tsaron Najeriyar ta fitar da sanarwa tana bai wa ‘yan Najeriya tabbacin tsaron dukiya da rayyukan jama’a, kuma tuni ta fara sintiri domin kara karfafa yanayin tsaro a birnin a sanarwar da kakin cibiyar yada labaru ta sojan Najeriyar Major General John Eneche mai kula da cibiyar yada labaru ta rundunar tsaron Najeriya ya bayyana.

Gwamnatin Najeriyar dai ta sha nanata bukatar nuna fahimta domin hada karfi kan yaki da Boko Haram  a kan halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar kamar yadda Dr Garba Abari Darakta Janar na hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriyar ya bayyana.

To sai dai ga Mallam Kabiru Adamu mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya yana ganin akwai kuskure kan yadda ake tafiyar da daukacin al’amarin.

Matsalar tsaro di ta yi kamari  a Najeriyar, to sai dai za’a sa ido a ga matakan sintiri da jami’an tsaron suka bayyana dauka a kan wannan batu da ke neman zama ruwan dare a kasar.