Fargabar yaki bayan kisan janar din sojan Iran a Iraki
January 3, 2020Farawa da cikin kasar ta Iraki, musamman ma a dandalin Tahreer,da ke tsakiyar birnin Bagdaza, yadda masu fafutukar neman sauyi a kasar suka kwashe makwanni suna gwaggwarmayar neman sauyi, wadanda kuma a karshen mako mayakan sa kai na Hizbullah ta Iraki suka nemi tarwatsasu amma a banza, masu zanga-zangar sun yi ta yin kuwar murna da shagulgula kan kashe Solaimanin da Amirkan ta yi, mutumin da suke dauka a matsayin babban dan kanzagin kasarsa ta Iran a kasarsu Iraki, wanda kuma yake kokarin kawo tangarda a yunkurin da suke na kawo sauyi, ake kuma zargin mayakansa da kashe tarin masu zanga-zanga:
"Irin wannan siyasar ta tsoma baki cikin lamuran kasarmu mun jima muna kashedi ga Iran da ta daina yi, domin ba za ta haifar mata da da mai ido ba.Solaimani ya zo kasarmu ne don neman lalata yunkurin neman sauyin da muke. Ko kuma don ya yi tasiri wajen sabon firaministan da ake shirin nadawa. Sai ga shi Allah ya hada shi da gamonsa, bayan da ya yi ta ingiza 'yan korensa suka far wa ofishin jakadancin Amirka. Irin wannan mungun tanadin da yake da shi da kasarmu ne ya sanya kake ganin muma muke mai da mummunan martani da wanna kisan da aka yi masa."
Shi kuwa shugaban addinin Iran, Ayatullah Ali Khamnaei, siffanta kashe Solaimanin ya yi da wani mummunan kuskuren da dole ne Amirka sai ta ciji yatsa kansa. Yana mai shan alwashin daukar fansa kanta ko ba dade ko ba jima.
A yayin da itama Hizbullah ta Irakin ta sha alwashin daukar fansa kan kashe babban kwamandanta da aka yi a yayin harin, a ta bakin Abdulhadi Muntasir, wani kusa na kungiyar:
"Wallahi sai mun dauko musu fansa. Daga yau Amirka ta kunna wutar da za ta kone ta. Za mu ci gaba da fafatawa da su ko mu yi nasara ko mu yi shahada.Wallah ba za mu taba barinsu haka ba."
Shi kuwa ministan harkokin wajen kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Qirqash, kira ya yi da a kai zuciya nesa, a kuma guji ci gaba da kada gangar yaki. Yana mai kira da a dauki matakan diplomasiyya da na siyasa don kashe wutar gabar.
Suma 'yan tawayen Al-Huthi na kasar Yemen, wadanda ke dasawa da Iran, kira suka yi ga kungiyoyin gwaggwarmaya da su hada karfi da karfe,don mai da mummunar martani cikin gaggawa kan kasar ta Amirka.