Fargabar yaki da Iran, Amurka na janye dakarunta daga Iraki
June 12, 2025
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan Amurkan da na Iran ke shirin ganawa a birnin Muscat na kasar Oman a karshen mako, a kokarinsu na dandalewa da cimma yarjejeniyar nukiliya, wacce shugaban Amurkan Donald Trump ke nuna tababa kan yiwuwar cimmata, har ya kaishi ga ba da umarnin janye manyan jami'an diplomasiyar kasar daga Iraki da fara janye dakarun sojinsa daga, gami da daukar matakan kandagarki a sauran sansanonin sojin Amurka da ke kasashen yankin Gulf.
"Dole ne mu janye mutanenmu daga wadannan wuraren da a yanzu ke da matukar hatsari.Domin zabin warware rikicin nukiliya da Iran ta hanyar diplomasiyya na dab da karewa, yadda za,a tilasta mu bin zabin anfani da karfin soji.Domin na riga na sha alwashin cewa, ba zamu taba barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba".
Amurka dai na da sansanonin sojinta a kasashen Qatar da Kuwait da Bahrain da Oman da ma Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda Iran tasha barazanar cewa, kansu zata fara kai farmakinta da zarar Amurka ta takaleta da yaki.
Wannan matakin da shugaba Trump na Amurkan ya dauka dai na zuwa ne, bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarhon da ya yi da firaiministan Isra'ila Benjamin Natenyahu, wanda ya zaku da ganin an kai wa Iran hare-haren ayit- ta-kare kan cibiyoyin bincikenta na nukiliya. Lamarin da ya sanya Natenyahun ke nuna jin dadinsa da sabon matakin na Amurka, wacce a baya tai ta gargadinsa da ya guji yin gaban kansa wajen kaiwa Iran hare hare,tun kafin matakan diplomasiya su gama gazawa wajen gamsar da ita kan cimma yarjejeniya.
"Sannu sannu ra'ayoyin kasashe masu 'yanci da son zaman lafiyar duniya na sake haduwa kan cewa, dorewar zaman lafiyar duniya na bukatar gaggauta lalalta shirin samar da nukiliyar Iran tun kafin a makara a fara cizar yatsa, bayan da dan tsako ya zama zakara".
Duk hakan dai na zuwa ne adaidai lokacin da kasar ta Iran ke barazanar sake bude sabbin tashoshin binciken nukiliya na asiri, biyo bayan zargin da tayi wa hukumar kula da bazuwar makamashin nukiiliya ta duniya da mika wuya bori ya hau ga bukatun kasashen yammacin duniya, wadanda suka nemi hukumar da ta hada rahoto da ke tabbatar da cewa, kasar ta Iran bata cika alkawuran da tayi wa hukumar na takaita tace sinadarin uraniyon kan bukatun fararen hula.
Kafin hakan dai, an jiyo jakadan kasar ta Iran a MDD, Amir-Saeid Iravanina gargadin cewa, kasar tasa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT ta hana bazuwar makaman kare dangi a duniya, bayan da kasashen Turai guda uku wato Jamus da Farana da Burtaniya suke son sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA.
"Kasar Iran tayi ta dagewa wajen bin matakan lumana don warware sabanin da ake damu kan cin moriyar makamashin nukiliya, don cimma yarjejeniyar da zata kai ga dage mana takunkumi. Duk da cewa bamu muka janye daga wannan yarjjeniyar a baya ba, mun yi mamaki yadda kasashen Turai da muka cimma wannan yarjejeniyar da su a 2015, a yanzu suke son sake farfado da wannan yarjejeniyar kafin wkarshen watan Otoba.Don haka gwanda mu rigasu daukar wannan matakin, duk da mun san hakan zai kara jawo dagula alakarmu da su".