1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin NATO akan 'yan tawayen Libiya

April 7, 2011

'Yan tawayen Libiya 10 ne suka mutu sakamakon harin da jiragen saman NATO suka ƙaddamar akan su

Wasu jiragen NATO a sansanin Sigonella dake kudancin ItaliyaHoto: dapd

'Yan tawaye da gwamnatin shugaban Libiya Muammer Gaddhafi sun bayyana cewar wani harin da dakarun ƙungiyar tsaron NATO suka ƙaddamar akan jerin gwanon motocin su a yankin gabashin Libiya wannan Alhamis, ya janyo mutuwar 'yan tawayen 10. 'Yan adawar dai sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewar matsalar ta afku ne a tsakanin birnin Ajdabiyya dake hannun 'yan tawayen da kuma Brega - mai arziƙin man fetur, inda 'yan adawa da kuma dakarun dake goyon bayan Gaddhafi ke ta fafatawa. 'Yan adawar suka ce 'yan tawayen da hatsarin ya rutsa da su dai - cikin kuskure ne suka je yankin, wanda a baya ma ƙungiyar NATO ta kaddamar da farmakin akan sa. A ranar Jumma'ar da ta gabata ce dai Jiragen yaƙin ƙungiyar NATO - cikin kuskure suka ƙaddamar da hari akan sansanin 'yan tawaye, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙa 13, kana wasu 11 kuma suka sami rauni, bayan zaton da NATOn ta yi cewar dakarun Gaddhafi ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou Madobi