Farmakin RSF a Port Sudan ya dauki hankalin jaridun Jamus
May 9, 2025
Jaridar Neuer Zürcher Zeitung ta yi sharhinta mai taken yakin Sudan ya kai wani mataki, inda ta ce a karon farko rikicin da ya halaka mutane kusan 150,000 ya kai ga birnin Port Sudan mai tashar jiragen ruwa da ake yi wa kallon tudun mun tsira. Jaridar ta ce rundunar sa kai ta RSF ta yi wa birnin Port Sudan luguden bama-bamai da jirage marasa matuka a ranar Lahadin da ta gabata. Daga cikin wuraren da hare-haren suka fada har da filin jirgin sama da sansanonin soji da tashar mai da kuma wani otel, lamarin da ya kai ga katse wutar lantarki yayin da hayaki ya turneke birnin.
Harin dai, wani mataki ne na kara dagulewar lamura a yakin Sudan wanda tun 2023 ya daidaita kasar ta uku mafi girma a Afirka. A bisa wasu kiyasi, yakin tsakanin dakarun sa kai na RSF da sojojin Sudan ya tilasta wa mutane fiye da miliyan 13 barin muhallansu. Harin jirage marasa matuka ya tilasta rufe filin jirgin saman birnin inda ta nan ne ake kai kayan agaji zuwa kasar Sudan.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana harin baya-bayan nan a matsayin mummunan lamari a yakin da ke ci gaba da gudana, kuma barazana ga fararen hula da ayyukan taimakon jin kai. Ko da a ranar Litinin, sojojin kasar sun fuskanci koma baya sakamakon wasu hare-hare na RSF: Rundunar sojin Sudan ta kai kara kasar Hadaddiyar Daular Larabawa gaban kotun duniya da ke Hague inda take zarginta da mara wa 'yan tawayen RSF baya wajen aikata kisan kiyashi. Sai dai kotun ta Hague ta ce ba ta hurumi a kan karar saboda kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye daga wasu sassa na kudirin yarjejeniya kan kisan kare dangi.
Yarjejeniyar Ruwanda da Amurka a jaridun Jamus
Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta ne kan yunkurin Ruwanda na cimma yarjejeniya da Trump domin a biya ta kudi ta karbi mutanen da Amurka za ta koro daga kasarta. Jaridar ta ce tsawon shekaru Amurka ta yi tana kokarin tasa keyar wani dan kasar Iraqi Omar Ameen, amma abin ya ci tura: Sai dai a karshe hakan ya yiwu a watan Maris da ya gabata.
A shekarar 2014 ne Ameen ya samu mafakar siyasa a Amurka, amma daga baya gwamnatin Iraqi ta zarge shi da yi wa kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS aiki inda suka halaka wani jami'in dan sanda, Ameen ya musanta zargin. Lauyansa ya yi gargadin cewa zai iya fuskantar hukuncin kisa a Iraqi ,a saboda haka wata kotu a Amurka a shekarar 2018 ta yanke hukuncin rashin mayar da shi Iraqi. Sai dai a yanzu cikin sirri ,an fiidda shi daga Amurka, sai dai ba kasar Iraqi aka mayar da shi ba, maimakon haka an kai shi ne kasar Ruwanda.
Omar Ameen, ba shi ne na farko dan kasar waje da gwamnatin sabuwar gwamnatin Amurka ta mayar da shi kasar da ba mahaifarsa ba. A tsakiyar wata Maris alal misali, Amurka ta mayar da 'yan Venezuella 238 zuwa gidan yarin El Savador da ya yi kaurin suna. Amma Ameen, shi ne na farko da Donald Trump a wa'adin mulkinsa na biyu ya tasa keyarsa zuwa kasar Ruwanda a gabashin Afirka, wadda a baya ta kasa daidaitawa da Birtaniya na karbar 'yan gudun hijira.
Ministan harkokin wajen Ruwanda Olivier Nduhungirehe ya tabbatar da cewar gwamnatinsu na tattaunawa da Washington don karbar 'yan gudun hijira daga wasu kasashe. Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa suna neman kasashe da za su karbi mutanen da ba sa bukata a Amurka.