Fashewar Bam a ƙasar Kenya
December 21, 2010Rahotanni na nuni da cewar kawo yanzu Mutane a kalla guda uku ne suka mutu yayin da wasu guda 23 suka tagayyara a sakamakom wani harin bam da aka kai a kan wata motar bus a tsakiyar Birnin Nairobi babban birnin ƙasar Kenya. Motar wacce ta ke tsaye a akan wani titi, bam ta fashe a cikin-ta a sa'ilin da ta ke ƙoƙarin tashi daga Nairobi zuwa birnin Kampala na ƙasar Yuganda. Ɗaya daga cikin fasinjoji da ya ke magana da gidan talabijin na ƙasar ya ce wasu mutane uku suka yi kutse a cikin motar, gabannin da wani jami'in tsaro ke bincikarsu su ka tada bam ɗin kuma daga cikin waɗanda suka mutu harda guda daga cikin su. Shugaban hukumar 'Yan sanda na Kenya ya ce a kwai alamun hannu 'yan ta'ada masu kishin Islama na ƙasar Somalia na ƙungiyar Al shabab, dake shirye-shiryen kai hare hare ƙunar baƙin wake a lokacin bukukuwan Krisimeti na wannan shekara.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar