1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu bama-bamai sun fashe a yankin Niger Delta

March 15, 2010

Ƙungiyar MEND ta ɗauki alhakin tada bama-bamai a lokacin taron sulhu a yankin Niger Delta

Fashewar bam a Niger DeltaHoto: picture alliance/dpa

Wasu bama-baman mota guda biyu sun tashi a birnin Warri dake yankin Niger Delta jim kaɗan bayan da ƙungiyar MEND tayi gargaɗin tada wasu bama-bamai a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters yace wannan bama-baman dai sun tashi ne a kusa da wani ginin gwamnatin Jihar inda ake gudanar da bikin dake da nasaba da wani shirin gwamnatin tarayya na kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a yankin na Niger Delta mai arzikin man fetur. kafin tashin bama-baman dai sai da ƙungiyar ta MEND ta aike da saƙwannin email ga kafofin yaɗa labarai game da harin wanda kuma sukace na tabbatar da ficewar ƙungiyar ta MENDS daga shirin gwamnan Malam Umaru Musa Yar'adua na kawo ƙarshen hare-hare a yankin, bayan samun cikas a shirin da rashin lafiyar shugaban ƙasar ya haifar.

Hare-haren da Ƙungiyar MEND ke kaiwa  a yankin Niger Delta sun kawo matuƙar cikas ga aiyukan haƙar man fetur a Nijeriya, lamarin kuma dake shafar kasuwanin mai na duniya.

Mawwallafi: Babangida Jibrin Edita: Halima Balarabe Abbas