1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar Cibiyoyin niukiliyar Japan

March 12, 2011

Gwamnatin Japan ta ce akwai yiwuwar cibiyoyin niukiliyar ƙasar sun fara tarwatsewa sakamakon girgizar ƙasar da ta afkawa ƙasar

Cibiyar niukiliyar Japan a yankin Fukushima gabannin girgizar ƙasa ta jiya Jumma'aHoto: AP

Hukumomi a ƙasar Japan na ƙara gano irin mummunan ta'adin da girgizar ƙasa da kuma ambaliyar ruwan da ta afkawa ƙasar a jiya Jumma'a suka janyo- yayin da gwamnatin ƙasar ke nazarin abubuwan da suka biyo bayan girgizar. Hukumar kula da ingancin cibiyoyin niukiliyar ƙasar ta Japan ta bayyana yiwuwar fashewar wasu abubuwa a cibiyoyin niukiliyar ƙasar guda biyu dake Fukushima, mai tazarar kilomita 250 arewa da Tokyo babban birnin ƙasar, inda hukumar ta ce akwai ma yiwuwar tuni ta'adin ya fara afkuwa ya zuwa wannan lokacin. Kafofin yaɗa labaran ƙasar ta Japan sun fara nuna alamun tarwatsewar wasu abubuwa tare da hayaƙin dake tashi a yankunan da tashoshin niukiliyar suke. Tashar telebijin ta gwamnatin Japan ta ruwaito cewar tuni rufin ɗakunan cibiyoyin suka tarwatse.

A halin da ake ciki kuma gwamnatin ƙasar ta Japan ta faɗaɗa yankunan da za ta sauyawa mutane matsugan su ya zuwa kilomita 20. Jami'an 'yan sanda a birnin Sendai, inda nanne ambaliyar ruwa sakamakon girgizar ƙasa ta ƙarƙashin teku ta fi yiwa ta'adi, sun sanar da cewar fiye da mutane dubu 70 ne suka rasa matsugunan su ya zuwa wannan lokacin, kana wasu fiye da 700 kuma suka rasu saboda girgizar ƙasa mai ƙarfin marki 8 da ɗigo 9 da ta afkawa ƙasar ta Japan a jiya Jumma'a. Akwai kuma wasu girgizar da suka biyo bayan wancan, amma basu kai ta farkon tsanani ba. Miliyoyin jama'a ne a ƙasar ba su da wutar lantarki da kuma ruwan sha sanadiyyar ɓarnar da girgizar ta janyo.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal