1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar sun mutu bayan taka nakiya

Ramatu Garba Baba MAB
May 8, 2023

Akalla sojojin Nijar bakwai aka tabbatar sun mutu bayan da motarsu ta taka nakiyar da aka dasa a kauyen Samira da ke yankin Tillaberi a yammacin kasar.

Nijar na fama da matsalar tsaro
Nijar na fama da matsalar tsaroHoto: AFP/S. Ag Anar

Rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar na cewa, wasu sojojin kasar bakwai ne suka mutu bayan da motar da jami'an tsaron ke ciki ta taka nakiya da ake zargin masu da'awar jihadi sun dasa a kan hanya. Lamarin na ranar Lahadin da ta gabata, ya auku ne a wani kauye mai suna Samira da ke yankin Tillaberi a yammacin kasar.

Sojojin Nijar na ci gaba da fuskantar barazana a sakamakon hare-hare, irin na kwanton bauna ko dasa nakiya ko ma bude musu wuta daga mayakan jihadi masu tsattsauran ra'ayin addini da suka hana zaman lafiya a kasar da ma kasashen Burkina Faso da Mali da ke makwabta da ita.