1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar nakiya ta kashe mutane a jihar Borno

April 13, 2025

Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane akalla takwas tare da jikkatar wasu da dama, sakamakon tarwatsewar wani abin fashewa da mota ta taka a hanyar Maiduguri zuwa Damboa a ranar Asabar.

Nigeria Besuch UN-Generalsekretär Guterres
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Mutanen yankin dai na zargin kungiyar  'yan ta'addan Boko Haram da kai harin a wani bangare na sabon yunkurin da take yi na sake dawowa da karfinta a jihar Borno.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ''mun samu rahoton abin da ya faru, kuma ina da yakinin cewa za a iya shawo kan wannan matsala. Za mu ci gaba da karfafa gwiwar al'umma, kuma ba za mu bari wannan al'amari ya hana zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Damboa ba. Ina kira ga Sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro da su ƙara tabbatar da tsaro a wannan hanya domin hana irin wannan harin a nan gaba.''

Harin ya sake jaddada matsanancin kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, yana kuma ƙara nuna bukatar ƙarfafa matakan yaki da ta'addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW