1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar tagwayen bama-bamai a Damascus

March 17, 2012

Fararen hula da dama suka mutu wasu kuma suka yi rauni bayan da bama-bamai suka fashewa a Damascus babban birnin Siriya

epa03148392 A handout photograph released by the Syrian Arab news agency (SANA) shows Syrian security officers inspecting the site of a bombing in Damascus, Syria 17 March 2012. Reports state that a number of civilians and Syrian security men died in two explosions targeting two intelligence centers, one targeted a building of security, criminal in the customs area and second in the region and targeted Air Intelligence Center in Kassa'a area in Damascus Syria. EPA/SYRIAN NEWS AGENCY SANA / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: SANA

Gidan talabijin na Siriya ya rawaito cewa fashewar wasu tagwayen bama-bamai ya kai ga hallakar fararen hula da 'yansanda 27 a yayinda wasu 97 kuma suka yi rauni. Shaidu sun ce maharan wadanda ake zargin sun yi amfani da kananan motoci, sun tinkari shelkwatar 'yan sandan da ke yaki da miyagun laifuka da kuma na jami'an leken asirin Siriya.

Wadannan hare-haren na kunar bakin wake sune matakan baya-baya nan da ake amfani da su, wajen nuna adawa da jami'oin sojin Siriya. Kuma irin wadannan hare-hare sun zama sanadiyyar mutuwar mutane da dama tun daga watan Disembar bara. Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin, to sai dai gwamnatin tana danganta shi da kungiyoyin ta'adda wadanda ta ke zargi da alhakin boren nuna kyaman gwamnatin da ke gudana a kasar. Manzo na musamman a sassanta rikicin Siriyar wato Kofi Anan ya ce dole ne a yi taka tsan-tsan wajen maida daidaito a kasar ta Siriya.

" I, duk da cewa mun mayar da hankali kan Siriya bai kamata a ce mun dauki wani mataki da zai ruruta rikicin ta yadda zai yi tasiri a yankin ba domin zai yi wahala a ciyo kan shi".

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal