1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masanan kimiyya sun lashe kyautar Nobel ta bana

Abdoulaye Mamane Amadou
October 7, 2025

Masanan kimiyya da suka yi bincike kan Physics sun lashe kyautar Nobel ta wannan shekara, bayan sun gudanar da bincike mai zurfi kan sinadarin quantum a kimiyyance

Hotunan masanan da suka gudanar da binciken kimiyya a bayan 'yan kwamiti masu bayar kyautar Nobe
Hotunan masanan da suka gudanar da binciken kimiyya a bayan 'yan kwamiti masu bayar kyautar NobeHoto: Jonathan Nackstrand/AFP

Masanan kimiyya uku ciki har da dan kasar Burtaniya sun lashe kyautar Nobel ta fannin Ilmin Physics a wannan shekara bayan da kwamitin bayar da kyautar ya yaba da bincike mai zurfi na kimiya da suka gudanar kan wani fannin kimiyya na quantum.

Masu yaki da makaman nukiliya sun lashe lambar yabo ta Nobel

Masanan kimiyar da suka hada da John Clarke dan Burtaniya da Michel Devoret na Faransa da Ba Amurke John Martinis sun samu kyautar ce bayan gano yadda sinadarin quantum ke tantance makamashi a cikin tsarin lantarki a kimiyance, kamar yadda kwamitin bayar da kyautar ya sanar a wannan Talata

Makamanciyar kyautar Nobel 2023

Kwamitin ya ce hanyar da aka yi amfani da ita ta kasance muhimmiya wajen gano sidanaren dake bunkasa sabbin hanyoyi na kimiyyar kantarki.