1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceAmurka

Iran: Fata bayan cimma yarjejeniya?

Suleiman Babayo LMJ
June 15, 2026

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani a kan yarjejeniyar tsagaita wuta, wadda aka cimma tsakanin Amurka da Iran da za ta janyo sake bude Mashigar Ruwan Hormuz.

Yarjejeniya | Sulhu | Iran | Amurka
Martani kan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da AmurkaHoto: Rainer Unkel/IMAGO

Har yanzu babu cikakken bayani game da kunshin yarjejeniyar da aka cimma, tsakanin Amurka da Iran din. Duk da haka ana batun fara aiki da yarjejeniyar, bayan saka hannu tsakanin bangaoririn biyu cikin wannan makon. Shugabanni da dama sun tattauna kan yarjejeniyar, tare da Shugaba Donald Trump na Amurka.

Kasashen duniya sun mayar da martani

Firaministan Birtaniya Keir StarmerHoto: Carlos Jasso/PA Images/picture alliance

Firaminista Keir Starmer na Birtaniya daya daga cikin jiga-jigan shugabannin ya ce, yana tsammani wannan yarjejeniyar tana da tasiri. Kasashen Faransa da Birtaniya sun bayyana cewa, suna shirye da taimakawa wajen sake bude Mashigar Ruwan Hormuz.

Karin bayani: EU ta jinjina wa Amurka da Iran kan amincewa da yarjejeniya

Kasashen Holland da Italiya ma suka amince da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran tare da fatan dorewarta. Kasar Chaina tana cikin wadanda suka mayar da martani kan yarjejeniyar, inda ta nuna fata wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar daga duk bangarorin biyu.

Firaministan Pakistan Shehbaz SharifHoto: Alexander Shcherbak/ZUMA/IMAGO

Sannan Chaina ta yi alkawarin aiki tare da kasashen duniya, wajen ganin samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Shi ma Firaminista Shehbaz Sharif na Pakistan da kasarsa ta taimaka wajen ganin an samu cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, ya gabatar da jawabin nuna jin dadi tare da jinjina ga bangarorin biyu.

Karin bayani: Pakistan ta mika wa Amurka martanin yaki kan Iran

Firaminista Sharif na Pakistan ya bayyana hakan ne, yayin jawabin da ya yi a gaban majalisar dokokin kasarsa. Ita ma Firaminista Sanae Takaichi ta kasra Japan ta nuna gamsuwa da tasirin wannan yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran. Ta nuna fata kan samun wucewar jiragen ruwa ba tare da wata matsala ta Mashigar Ruwan Hormuz da samun yarjejeniya ta karshe da za ta gamsar kan batun nukiliyar Iran.

Fatan sake bude Hormuz

Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Chris Emil Janssen/picture alliance

A ranar Jumma'a 19 ga watan Yuni na 2026, ana sa ran saka hannu kan yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran da za a yi a birnin Geneva na kasar Switzerland. Ana sa bangaren Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya ce, kasarsa za ta ci gaba da daukar matakan kare kanta.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani