Duniya na tir da mamayar Rasha a Ukraine
October 13, 2022Talla
Kasashe 143 daga cikin kasashe 193 na duniya sun kada kuri'ar amincewa da kudurin yin tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, yayin da kasashe 35 suka ki amincewa da shi ciki har da Rasha da Siriya da Nicaragua da Koriya ta Arewa da Belarus.
Bisa ga dokokin kasa da kasa dai ba dole ba ne a aiwatar da kudirin, amma ya nuna yadda Moscow ke zama saniyar ware a duniya. Har ila yau kudurin ya sake tabbatar da 'yancin kai da walwala na Ukraine a kan iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.