Brazil ta ce a kai kasuwa taimakon kudin daga G7
August 27, 2019Talla
Da yake mayar da maratani ga matakin tallafin jim kadan bayan kammala taronsu a birinin Biarritz na kasar Faransa, darakatan fadar shugaban Brazil ya cewa tayin tallafin akai kasuwa, inda ya caccaki shugaba Emmaneul Macron na Faransa da ya bayyana sanarwar agajin kudin, yana mai cewa da ya mayar da hankalinsa ga kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka maimakon Brazil, kana kuma ya ce ta kaka shugaban da ya kasa daukar matakin hana gobara a majami'ar Notre Dame, zai ba da wani misali ga kasar ta Brazil.