1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan tattaunawa don kawo karshen rikicin Sudan

Mahmud Yaya Azare
January 9, 2024

Takaddama a ganawa tsakanin manyan jagororin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan da Janar Mohammad Hamdan Dagalo,dangane da sharuddan ganawarsu da juna don shiga tattaunawar kawo karshen yakin

Kombobild Abdul Fattah Al-Burhan und Mohamed Hamdan Dagalo
Hoto: Bandar Algaloud/Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Duk da mummunar asarar da sojojinsa ke tafkawa da ta hada ga rasa manyan garuruwan da ke da matukar muhimmanci a bangaren tattalin arziki da dabarun yaki, shugaban rundunar sojin kasar Sudan janar Al-Burhan wanda a yanzu ya karkata ga tayar da tsimin mayakan haula da kabilun kudanci da Gabashin Sudan su dauki makamai don kare abun da ya kira "diyauci da mutuncin Sudan na ci gaba da jan kafa wajen amsa tayin da madugun yan tawayen kasar, shugaban rundunar sojin sai kai na RSF yayi masa, na dakatar da yaki nan take da shiga tattunawar sulhu don dawo da zaman lafiya a kasar.

Karin Bayani: Sudan: Mayakan RSF sun shiga Wad Madani

Janar Abdel Fattah al-Burhan na SudanHoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

"Yanzu ba lokacin tattaunawa bane, lokaci ne na sake damara don tunkarar makiya al'ummar Sudan. Babu batun shiga tattaunawa ko ganawa da wadanda suka ci amanar kasa, muddin basu juya baya ga burinsu na mulkar kasar Sudan karfi da yaji ba, basu kuma yi watsi da aiwatar da mungun shirin kasashe makiya Sudan da ke neman wargazata don sace arzikinta ba. Sharadinmu na shiga tattunawa da su shi ne, su fice daga cikin gidajen mutanen da suke mamaye dasu, su kuma janye dakarunsu daga jihar Al-jazeerah da suke ci gaba da cin zarafin mutanenta, kana su koma ga yin aiki da yarjejeniyar birnin Jedda da ta haramta ci gaba da baza mayaka a wuraren da ake zaman lumana, idan ba haka suka yi ba, to za mu ci gaba da yakarsu, mu kadai ba sojojin haya babu tallafin wasu kasashen ketare, mu kadai al'ummar Sudan.”

Karin Bayani: MDD ta ce yakin Sudan ya jefa mutane miliyan 18 cikin halin tsananin yunwa

Wannna martanin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen da ada suka nuna suna tare da janar Al-Burhan din musammam kasashen Masar da Saudiya da Qatar, suka yaye masa baya, bayan da suka ki bashi karin makamai, don tsoron tsawaitar yakin, lamarin da ya sanya janar Al-Burhan din sake shirin yin rangadi ga wadannan kasashe don gamsar da su muhimmancin bashi isassun makamai.

Sudan | Mohamed Hamdan DagloHoto: Rapid Support Forces/AFP

Masharhanta dai na nuna fargabar tsundumar kasar Sudan cikin yakin basasar da ba a san karshensa ba, muddin bangarorin biyu za su ci gaba da fakewa da mutanen gari wajen kiransu su dauki makamai, don shiga yakin da aka yi amannar cewa, jagogorirnsa na yi ne don kwadayin mulki ba don kishin kasa ko kyautata rayuwar talakawan kasar ba.

Kafin hakan dai, madugun yan tawayen na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda yayi rangadi a kasashen gabashin Afirka, wanda kuma aka yi ammanar yana samun tallafi daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa don ya murkushe mata kungiyar Yan Uwa Musulmi da suka yi mulki karkashin hambararren shugaban kasar Umar Al-Bashir da kansa ya mika bukatar tattaunawar don samar da zaman lafiya a kasar wadda yaki ya daidaita: