1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan 'yan Lebanon ga sabon shugaba Joseph Aoun

Mahmud Yaya Azare
January 10, 2025

Al'ummar Lebanon na ci gaba da bayyana fata ga sabon shugaban kasar Joseph Aoun wanda aka zaba.

Sabon shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun
Sabon shugaban kasar Lebanon Joseph AounHoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Dubban mutane a garuruwan Lebanon sun fito kan tituna dauke da tutocin kasar don murnar nasarar zaben sabon shugaban kasa.

'Yan kasar dai sun  baiyana fatan shugaban zai gaggauta nesanta kasar daga rikice rikicen da katsaladan na kasashen ketare a cikin al'amuran kasar. Sun bukaci ya mayar da hankali kan gina kasar da yan kasa yadda Lebanon za ta zama abar alfahari ga duniya.

Wasu 'yan kasar da ke daukar kungiyar Hizbullah a matsayin wadda ke jawo wa kasarsu masifa ga abun da suke cewa:

Hoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

"Hakika kowane lokaci muna bukatar daukar matakan da suka dace. A wannan matakin ba ma so a sake barin Hizbullah ta fi rundunar sojin Lebanon karfin makamai. Bai dace a bar wasu suna daukar makamai idan ba sojoji da aka dora wa alhakin kare kasa ba.”

Wasu kuwa bukatarsu shi ne gaggauta kyautata yanayin tattalin arzikin kasar da ya jima da durkushewa:

"Muna taya shi murnar zabinsa da aka yi. Allah ya yi masa jagoranci a kyawawan manufofinsa musamman alkawarin farfado da tattalin arziki da maido da 'yan yawan bude ido da suka kaurace wa kasarmu. Yin haka ne kadai zai hana watangaririyar samari kan tituna da shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin gida da ketare, saboda 'yan kudaden da ake basu don rashin aikin yi.”

Hoto: Bilal Hussein/AP/picture alliance

 Ita kuwa gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na kasar, wadanda suka yi tsayuwar daka wajen matsin lamba ga 'yan majalisun kasar su tabbatar da an yi nasarar gudanar da zaben shugaban kasa a wannan karon, bayan doguwar dambaruwar da ta jefa kasar zama kusan shekaru uku ba tare da shugaban kasa ba. 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani